SHUGABA BAWAN AL’UMMA
MANEMA LABARAI
Karamar Hukumar Rimin Gado, Kano
27/4/2025
A ci gaba da kokarinta na inganta harkokin ilimi a karamar hukumar Rimin Gado, shugaban karamar hukumar, Hon. Sani Salisu, ya amince da gina sababbin ajujuwa guda 12 tare da gina bandakuna na musamman (VIP Toilets) a wasu makarantu.
Ga jerin makarantun da za a gina musu bandakuna na musamman:
1. Dan Shayi Primary School
2. Karofin Yashi Primary School
3. Juji Primary School
4. Rimin Gado Special Primary School
5. Yalwa Primary School
Sannan kuma, ga jerin makarantun da za a gina musu sababbin ajujuwa:
1. Yangu Primary School
2. Dugurawa Primary School
3. Jambulo Primary School
4. Riga Gulu Primary School
5. Ingali Mai Gari Primary School
6. Dan Isah Nomadic Primary School
Wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin karamar hukumar na bunkasa walwalar dalibai da malamai a fadin Rimin Gado.
Sahannun:
Arribbabatu Sani Yakasai
Jami’ar Yada Labarai,
Karamar Hukumar Rimin Gado.
Leave a Reply
Want to join the discussion?Feel free to contribute!