LABARANMU A YAU

“GWAMNATIN KANO ZATA CIGABA DA RABA GANIMAR YAQI DA WA”DANDA AKAI YAQI DA SU”

Babban mai bawa gwamnan jihar Kano Shawara a harkokin siyasa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke jawabi ga ‘yan Kasuwa na jihar Kano masu ra’ayin KWANKWASIYYA.

Alhaji Sunusi ya ce akwai kananan ‘yan Kasuwa an sansu a tantancesu a taimaka musu, da ‘,yan Kasuwa masu Kasa kaya da sukai yawo da motocinsu sukai ta Samun barazana ta za ‘a ka ma su.

“Duk sanda zamuyi Taro Sai an turo Jami an tsaro masu saka farin kaya (SS) domin a kama mu Sai ni zanyi musu waya mu can za wajen taron.”Kotun koli ya jaddada.

Alhaji Sunusi ya ce a cikin jerin ‘yan kungiyoyi kimanin dubu Tara da dari Tara da sittin da uku (9,963) da Ake da su ba wadanda bai sa ni ba,kuma ba wani taro da akai na ‘yan Kasuwa da bada shi akayiba,saboda haka duk wanda ya taimaka ya san shi.

Ya kuma ce gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf mai tausayi ne,mai jinkai zai cigaba da kulawa da wadanda su ka bada gudun mawa wajen samun nasarar kafa Gwamnatinsu.

Ya gode musu ya kuma ba su tabbacin cigaba. da bawa duk wasu kungiyoyi hadinkai da za,a nema ta ofishinsa wajen taimakawa Al’umma, domin dorewar nasarar Jamiyyar NNPP Kwankwasiyya a Kano dama Kasa baki daya.

Da ya ke jawabi a madadin’yan kungiyar Babban Sakataren kungiyar , Aminu Salisu na (Uku),ya bayyana makasudin zuwansu, ya kuma godewa mai Girma gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya zabo jajirtacccen mai bashi Shawara a harkokin siyasa.

Sahannu:
Aminu Sani Ali( P.R.O)
28 April 2025

0 replies

Leave a Reply

Want to join the discussion?
Feel free to contribute!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *