PRESS         RELEASE

MADOBI LOCAL GOVERNMENT AREA

28/04/2025

ZAMU CHIGABA DA INGANTA HARKOKIN LAFIYAR ALUMMARMU MASAMMAN RIGAKAFIN YARA KANANA DA MATA MASU JUNA BIYU SABO DA MAHIMMANCHISU INJI SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR MADOBI SULEIMAN DAN AZUMI.

Shugaban Karamar Hukumar madobi AlhajI
Suleiman Dan Azumi ya bukachi iyayen Yara dasu cigaba da bawa Hukumomin Lafiya hadin kai da goyan baya na ganin anyiwa yaran su Alluran Rigakafin Shan inna da sauran rigakafin da ya dace na inganta Lafiyar yaran  a yankin.

Yayi wannan kiranne ayayin da yake kaddamar da Alluran Rigakafin Shan inna na zagayan farko a shekararnan ta 2025 Wanda ya gudana a Garin Koyan gidan ayu dake Karamar Hukumar ta Madobi, Inda ya bayyana jindadinsa bisa irin yadda suke samin hadin kai da goyan baya daga iyayen yara da Hukumomin Lafiya a amatakai da ban da ban tarayya, jaha, who, unicef, Health for Africa da sauransu.

Suleiman Dan Azumi Shugaban Karamar ya kara da cewa zasu chigaba da bawa harkokin Lafiya mahimmanchin da ya dace a yankin wayanda suka hada da mata masu chiki da harkokin rigakafin yau da kullun da sauran yaki da laruralarure akan inganta Lafiyar jamaa.

Anata jawabin shugabar Sashin Lafiya a matakin farko Hajiya Wasila Mohammad usuman tayi bayani mai tsaho akan mahimmanchin rigakafin Alluran shan inna ga Yara kanana yan kasa  da shekaru Biyar don cigaban Lafiyarsu, Da zuwa awo ga Mata masu juna Biyu dan a asami raguwar macemacensu ayayin hayhuwa.

Shugabar Sashin Lafiyar wasila usuman tace anasa rai zaayiwa Yara yankasa da shekara Biyar Alluran Rigakafin su kimanin Dubu saba, in da za aiwa (70.000)a yankin zuwa ranakun da aka ware na gabatadda aiyukan rigakafin.

Da suke nasu jawaban da ban da ban jami i mai kula da wayar da kan Alumma a kan harkokin Lafiya na yankin Alhaji Mustapha A Nura da wakilan Hukumomin Lafiya na Duniya WHO, da UNICEF, E HEALTH for AFRICA Wanda Hajiya Amina Hamza ta wakicesu ta WHO sun jaddada mahimmanchin rigakafin chutar shan inna da sauran rigakafin yau da kullun ga kananan yaran da basu wuce shekara Dayaba, Sannan sun godewa Hukumomi da iyayen kasa dan gane da irin hadin kan da suke samu na gabatadda shirin Cikin nasara.

Ajawabinsa Hakimin Madobi majidadin kano Alhaji Musa sale Musa Kwankwaso ya jaddada goyan bayan masarautarsa na cigaba da yin aiki tukuru na ganin ansami nasarar da ake da Bukata na inganta Lafiyar yaranmu da sauran Alummar yankin.

Daga karshe Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Suleiman Dan Azumi ya duba yadda ake gudanar da aikin a yakun Cikin Garin, da gabatadda zaman bada baya nai akan aiyukan rigakafin( wato evening meeting report
) a ofishinsa dake asakatariyar Karamar Hukumar ta Madobi.

Sa hannu

Daga Jamien yada labarai na Karamar Hukumar ta Madobi.
Yusuf Sabo

0 replies

Leave a Reply

Want to join the discussion?
Feel free to contribute!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *