SANARWA GA MANEMA LABARAI
24 ga Yuni, 2025

HUKUMAR KYAUTATA DAAR MAAIKATA DA INGANCIN AIKI (SERVICOM) TA GUDANAR DA ZIYARAR BA-ZATA GA MAAIKATU DA HUKUMOMIN JAHAR KANO DON HANA MAKARA DA INGANTA KYAKKYAWAR DABI’A A CIKIN AIKIN GWAMNATI

A wani salo na kokarinta na inganta yadda ake gudanar da ayyuka da kuma kara daidaito a cikin aikin gwamnati na jiha, hukumar SERVICOM bisa jaorancin Darakta Tahir Garba ta gudanar da ziyarar ba-zata zuwa wasu Ma’aikatu, Sassa, da Hukumomi (MDAs) a cikin babban birnin jihar. Wannan yunkuri na nufin hana makara zuwa aiki da kuma magance wasu dabi’u da halaye marasa kyau da ke hana ingantaccen aiki a bangaren gwamnati.

Wannan bincike na ba-zata, wanda ya zo wa MDA da dama a bazata, an tsara shi ne domin duba halin shigowa aiki da wuri, halin halartar ma’aikata da kuma yadda suke gudanar da kansu a wajen aiki. Wannan ziyara kuma ta kasance wata tunasarwa ga ma’aikatan gwamnati kan muhimmancin gaskiya, jajircewa, da daukar nauyin aiki yadda ya kamata.

A lokacin ziyarar, Babban Sakatare na Ma’aikatar Kudi ya yaba da kokarin SERVICOM, ya bayyana aikin su a matsayin “aikin hakuri.” Ya ce duk wanda ke kokarin gyara kura-kurai a cikin tsarin gwamnati, dole ne ya shirya fuskantar rashin fahimta ko kuma rashin karbuwa, musamman idan ana kalubalantar halaye mara sa kyau da suka dade ana yi. Ya ce, “Kiran mutane zuwa ga ladabi da daukar nauyin abin da suke yi ba abu ne mai sauki ba, amma dole ne idan har muna son mu ci gaba da bunkasa hukumominmu.”

Ya kuma bayyana damuwa game da yadda wasu malamai ke tafiya da ‘ya’yansu zuwa makarantu masu zaman kansu kafin su wuce wurin aikinsu, wanda hakan ke sa su makara. A cewarsa, wannan dabi’a ba wai kawai tana nuna mummunan misali bane, har ma tana rage ingancin aiki a wuraren aiki. Ya jaddada cewa dole ne a dauki matakin gaggawa kan irin wannan hali idan har ana son dawo da amincewar jama’a ga aikin gwamnati.

A Hukumar Binciken Kudaden Jihar, tawagar SERVICOM ta lura da rashin isassun ma’aikata a ofis. Sai dai shugaban sashin ya bayyana cewa yawancin ma’aikatan su suna ayyukan waje (field work), don haka ba sa yawan kasancewa a ofis a lokacin aiki. An karbi wannan bayani, amma ta jaddada muhimmancin daidaita tsakanin ayyukan waje da na ofis.

A daya bangaren, Ma’aikatun Yada Labarai, Kudi, da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) sun nuna babban matakin halartar aiki. A lokacin ziyarar, mafi yawan daraktoci da manyan ma’aikata suna wurin aiki kuma suna cikin ayyukansu, wanda hakan ke nuna jajircewa da kishin aiki.

SERVICOM ta yaba da irin wadannan ma’aikatu bisa kyakkyawar dabi’arsu, tare da kira ga sauran su yi koyi da su. Ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da gudanar da irin wadannan ziyarce-ziyarce ba tare da sanarwa ba a matsayin wani bangare na tabbatar da bin ka’idojin aiki da kuma samun ingantaccen aiki a gwamnati.

SERVICOM na kira ga dukkan ma’aikatan gwamnati da su dauki aikinsu a matsayin hidima ga al’umma, su kuma kasance masu rikon gaskiya, shigowa da wuri, da kuma nuna kwarewa a duk ayyukansu. Al’umma na da hakkin samun ingantacciyar hidima, kuma hakan ba zai yiwu ba sai duk jami’an gwamnati sun dauki aikinsu da muhimmanci.

Ziyarar ba-zata za ta ci gaba a sauran hukumomi a cikin makonni masu zuwa.

Sanyawa hannu:
Jamil Sagir Danbala
Jami’in Hulda da Jama’a, Direktaret din SERVICOM, Kano

0 replies

Leave a Reply

Want to join the discussion?
Feel free to contribute!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *