MANEMA LABARAI
22 Ga Yuli, 2025

HUKUMAR KYAUTATA DAAR MAAIKATA DA INGANCIN AIKI SERVICOM TA JIHAR KANO TA CI GABA DA ZIYARAR BA-ZATA DOMIN INGANTA AIKIN BAYAR DA HIDIMA

A ci gaba da jajircewarta na ganin an inganta gaskiya, kwarewa da ingancin aiki a hukumomin gwamnati, Darakta Tahir Garba, shugaban Hukumar SERVICOM na Jihar Kano, ya jagoranci ziyarar ba-zata zuwa wasu Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) domin tantance yadda ake gudanar da ayyuka a fadin jihar.

Lokacin da tawagar ta kai ziyarar zuwa Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine, sun nuna gamsuwa matuka da kyakkyawan aikin gine-gine da ake aiwatarwa, wanda Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ke jagoranta. Darakta Tahir Garba ya yaba da hangen nesa da jajircewar Gwamnan wajen kawo ci gaba, yana mai cewa wannan aikin ya nuna cikakken niyyar gwamnati na kyautata rayuwar al’umma.

Sai dai kuma, ziyarar ta bayyana wasu kurakurai wajen halartar aiki a wasu wuraren. Babu ko ma’aikaci daya da aka tarar da shi a bakin aiki a lokacin ziyarar a:

Asusun fansho na Jihar Kano (State Pension Trust Fund)

Ma’aikatar Raya Karkara da Ci gaban Al’umma

Haka kuma, ‘yan ma’aikata kalilan ne kawai aka samu a:

Hukumar Ruwa ta Jihar Kano

Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine, Kano Geographic Information System (KANGIS)

Kano State Senior Secondary Schools Management Board (KSSSSMB), Daraktaren Ilimi na Yankin Birni (Municipal Zonal Education Directorate)

Hukumar Kula da Makarantun Allo da Islamiyya (Kano Quranic and Islamiyya Schools Management Board)

Darakta Tahir Garba ya jaddada cewa manufar wadannan ziyarce-ziyarcen ba wai hukunta kowa bace, sai dai karfafa aiki da kishin kasa, tare da tabbatar da cewa kowane ma’aikaci yana aiwatar da aikinsa yadda ya kamata. Ya bukaci ma’aikatan gwamnati su riƙa zuwa aiki akan lokaci da cikakken sadaukarwa. Ya kuma tabbatar da cewa ziyarce-ziyarcen bazata za su ci gaba da gudana domin tabbatar da anayi wa jama’a aikin da ya dace.

Sa hannu:
Jamil Sagir Danbala Jamiin Hulda da Jama’a
Na Hukumar kyautata daar maaikata da aiki SERVICOM, Jihar Kano

0 replies

Leave a Reply

Want to join the discussion?
Feel free to contribute!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *